Gwamnatin mulkin sojin kasar Nijar ta bukaci kamfanonin kasar Rasha da su shigo kasar domin zuba jari a fannin ma'adanin Uranium da sauran albarkatun da kasar ke da su.
Ministan ma'adanai na kasar Ousmane Abarchi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba.
Rukunin kamfanin Orano na kasar Faransa ya dakatar da aikin hakar Uranium a watan da ya gabata, biyo bayan tsamin dangantaka tsakanin sa da gwamnatin mulkin sojin kasar.