Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano ta ce ta bankado wani wurin ajiye kaya da a ke zargi da sauya buhuhuwan shinkafar da gwamnatin tarayya ta bayar domin rabawa mabukata.
Shugaban hukumar Barrista Muhuyi Magaji, ya ce a yayin wani samame da suka kai a wurin ajiye kayan dake unguwar Hotoro, sun gano shinkafar da ta kai mota 28 da suke zargin an karkatar da akalarta ne domin sake yi mata mazubi a sayar a kasuwanni.
Ya ce sun kama wani mutum daya kuma ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano wadanda su ke da hannu a wannan abin, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
Category
Labarai