Hukumar kwastam a Nijeriya ta tara kudaden da yawansu ya kai tiriliyan 2 a tashar ruwa ta Apapa dake Lagos.

 







Hukumar kwastam a Nijeriya ta tara kudaden da yawansu ya kai tiriliyan 2 a tashar ruwa ta Apapa dake Lagos. 


Hukumar hana fasakauri ta kasa (Custom) ta ce jami’anta da ke aiki a tashar jiragen ruwa da ke Apapa a jihar Lagos sun tara kudaden shiga da yawansu ya kai kimanin Naira tiriliyan biyu 2. 


Shugaban hukumar na yankin, Kwanturola Babatunde Olomu, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi a yayin wani fareti da jami'an kwastam su ka gudanar  a ranar Laraba a jihar Legas.


Mista Olomu ya ce hukumar na son cimma muradinta na samun tiriliyan 2.2tr kafin karshen Disamba na  wannan shekarar.


Ya ce rundunar ya bayyana cewa hukumar ta yi nasarar tattara kashi 40 na jimillar kudaden da hukumar ta tara da a fadin kasar zuwa yanzu da suka kai naira tiriliyan 5.07.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp