Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ICPC ta soma bin diddigin wasu ayyukan ci gaban al'umma na mazabun 'yan masalisa da na kananan hukumomi a jihar Kano domin tabbatar da bin ka'ida
Ayyuka 99 ne za ayi a mazabun 'yan majalisa, sai wasu manyan ayyuka bakwai a kananan hukumomi 44 na jihar, wadanda za su lakume kudaden su suka kai naira biliyan 41.
Shugaban hukumar ICPC a Kano Barista Ibrahim Garba Kagara, ya ce za su sanya ido akan yadda za a gudanar da ayyukan domin tabbatar da cewa ba a aikata wata almundahana ba, kuma an gudanar da su kamar yadda aka tsara domin amfanin al'umma.
Hakama ya bukaci al'ummar da za a yiwa wadannan ayyuka da su sanya ido kuma su kai rahoton duk wata rufa-rufa ko badakala da suka ga ana shirin aikatawa.