Hukumar tattara haraji ta jihar Kano ta rufe babban ofishin kamfanin jiragen sama na Max Air saboda gaza biyan harajin sama da naira miliyan 190 daga shekarar 2012 zuwa 2017.
Hakama hukumar ta garkame ofishin gine-gine "Dantata and Sawoe Construction" saboda kin sakawa gwamnati kudin harajin da ya kai miliyan 241.
Daraktan kula da basussuka na hukumar Madam Ibrahim Abdullahi, ya ce kamfunnan sun ki amsa sakon da hukumar ta aike musu, wannan ne ya sa ta nemi izini daga kotu domin kullesu.
Category
Labarai