Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya EFCC za ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello a gaban babbar kotun tarayya dake Abuja a yau.
Za a gurfanar da Yahaya Bello ne tare da wani makusancinsa da wasu mutum biyu Dauda Suleiman da kuma Abdulsalam Hudu, a gaban Mai Shari'a Emeka Nwite a kan zarge-zarge 19 na badakalar kudi naira biliyan 80.0.
Ko jiya Alhamis, sai da hukumar ta gurfanar da Yahaya Bello ne tare da wasu mutane biyu akan zarge-zarge 16 wadanda suka musanta aikatawa.
Category
Labarai