Hukumar jin dadin alhazzai ta jihar Sokoto ta ce ta samu kujeru 6000 daga hukumar alhazzai NAHCON ta kasa domin sayarwa maniyyata aikin hajjin 2025 a jihar.
Shugaban hukumar Alhaji Aliyu Musa, a lokacin taron manema labarai da ya gudanar, ya bada umurnin ajiye naira miliyan 8.4 ga duk mai niyyar zuwa aikin hajjin bana.
Ya ce tuni jihar Sokoto ta soma shiri domin tunkarar aikin hajjin na shekara ta 2025, ta hanyar sayar da kujerun aikin hajji.
Sai dai Alhaji Aliyu Musa ya bayyana cewa hukumar alhazzai ta kasa za ta iya sake bitar farashin kujerar idan an samu karin kudi ko kuma ragi.
Dangane da samun nasarara aikin, shugaban hukumar alhazzan Sokoto ya ce sun dauki darasi daga kalubalen da suka fuskanta a shekarar da ta gabata kuma zasu yi kokari kauce musu.