Hedikwatar tsaron Nijeriya na neman karin wasu 'yan ta'adda ruwa jallo


Mutanen da ake nema ruwa a jallo sun hada da Abu Khadijah, Abdurrahman, Dadi Gumba, Abu Muhammed, Usman Kanin Shehu, Abu Yusuf, Musa Wa’a, Ibrahim Suyeka, BA Sulhu da Idris Taklakse.


Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da babban hafsan sojin kasar ya tabbatar da bullar wata sabuwar kungiyar ta’addanci da aka fi sani da ‘Lukarawas,’ wanda ke kara ta’azzara matsalar rashin tsaro a yankin arewa maso yammacin Nijeriya.


Daraktan yada labaran hedikwatar tsaro, Maj Janar Edward Buba, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan ayyukan rundunar a ranar Alhamis a Abuja.


Ya ce sabuwar kungiyar ta'addancin ta bulla ne daga Jamhuriyar Nijar bayan juyin mulkin da ya kai ga rugujewar hadin gwiwar sojoji tsakanin Nijeriya da Nijar din.


Ya kara da cewa 'yan ta'addan sun fara kutsawa cikin yankunan arewacin jihohin Sokoto da Kebbi daga jamhuriyar Nijar da Mali, musamman bayan juyin mulkin da aka yi.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp