Jami’in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar DSP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wani bayani da ya fitar.
A cewar sa, wata mota ce kirar Toyota bus ta fada a kan wata Tirela dake ajiye.
DSP Lawan ya ce direban motar da mutum tara sun riga mu gidan gaskiya, yayin da mutun daya ya tsira da rauni.