Gwamnan Bauchi Bala Muhammed |
Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya sake duba kudirin gyara harajin da aka tsara kwanan nan, inda ya bukaci a sake duba shi tare da mai da hankali kan hadin kai ga kasa.
Ya yi kira ga shugaban kasa da ya dakatar da ci gaban kudirin gyaran harajin tare da karbar shawarwari masu yawa don tabbatar da adalci da daidaito kafin a zartar da shi a matsayin doka.
Musamman yadda kudurin ya haifar da kakkausar suka daga gwamnonin Arewa da masu masarautun gargajiya. Amma duk da hakan shugaban ya yi watsi da kiraye-kirayen janye kudirin.
A lokacin da yake hira da Sashen Hausa na BBC, Gwamna Bala ya yi gargadin cewa shirin sake fasalin harajin zai kara tabarbare tattalin arzikin da yawancin jihohin arewacin kasar ke fuskanta.
Gwamna Mohammed ya yi bayanin cewa jihohin arewa, wadanda da yawa daga cikinsu sun riga sun fuskanci kalubalen kudi, kuma za su kara samun tabarbarewar tattalin arziki sakamakon sabon tsarin harajin idan aka tabbatar da shi.