Gwamnatin shugaba Tinubu ta gargadi sabbin ministocin ta kan su guji kabilanci da bangaranci, ta kuma shawarce su da su fuskanci ayyukan da ke gaban kasa.
Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ne ya yi wannan gargadin a Abuja a wajen bude taron kwana biyu da ofishin sa ya shirya wa sabbin ministocin.
A ranar Litinin din da ta gabata ne dai shugaba Bola Tinubu ya rantsar da sabbin ministocin guda bakwai a fadar sa da ke Aso Rock Villa.