Shugaban hukumar kidayar jama'a ta kasa Nasir Isa Kwarra, ya bayyana cewa za a gudanar da aikin kidayar jama'a a cikin shekara ta 2025.
Kwarra ya bayyana haka ne a wurin taron bita da aka gudanar a Abuja, kan babban taron kasa da kasa na yawan jama'a da ya gudana a Nairobin ƙasar Kenya.
Idan za a iya tunawa, gwamnatin da ta gabata ce ta dakatar da aikin kidayar jama'a wanda aka tsara yi a shekarar 2023.
Category
Labarai