Gwamnatin Nijeriya za ta gina kananan tashoshin samar da lantarki a jami'o'i

 Gwamnatin Nijeriya ta sanar da shirin samar da sabbin kananan tashoshin samar da hasken wutar lantarki masu amfani da hasken rana a harabar manyan makarantu da asibitocin koyarwa a fadin kasar don rage tsadar wutar lantarki


Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana haka a lokacin da yake duba aikin Advanced Solar Microgrid a Jami’ar Abuja, wanda ya ce an kammala kashi 95 cikin 100.


Ya ce kirkirar wadannan kananan tashoshi zai taimaka sosai wajen ganin an kawo karshen tsaiko da matsalar lantarki da ake fama a wuraren 


Nijeriya dai fama da matsalar lalacewar lantarki a sakamakon yawan samun matsala da babbar tashar samar da lantarki take yi lokaci zuwa lokaci.


Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp