Gwamnatin Nijeriya za ta dawo da harajin saukar jiragen 'Helicopter' na $300 a filayen jiragen kasar


Hukumar kula da iyakokin sama na Nijeriya ta ce za ta soma karɓar harajin saukar jiragen 'Helicopter' na dala 300 a filayen jiragen kasar nan ba da jimawa ba.

Wannan na zuwa ne watanni shida da gwamnatin tarayya ta dakatar da harajin saboda kin amincewar kamfunnan jiragen sama.

Da yake jawabi a wurin babban taron kungiyar ma'aikatan jiragen sama, darakta mai kula da sufurin jiragen sama na hukumar Mista Tayo John, ya ce ta hanyar karɓar haraji za su magance kalubalen kudaden da suke fuskanta.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp