Shugaba Tinubu |
Ministar harkokin mata, Imaan Sulaiman-Ibrahim, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba a Abuja domin tunawa da ranar yara ta duniya.
Ana bikin ranar yara a kowace shekara a duniya a ranar 20 ga Nuwamba, kuma rana ce da majalisar dunkin duniya ta ware domin 'yancin yara.
Sakamakon haka, majalisar dinkin duniya ta yi bikin a wannan rana tare da kokarin wayar da kan al'umma game da muhimmancin ilimin yara, kula da lafiyar su da kuma bukatar magance matsalolin da yaran ke fuskanta.
Ministar harkokin mata, don haka ta ce gwamnati ta himmatu wajen samar da yanayin da kowane yaro zai samu ilimi da lafiya da rayuwa ingantacciya ba tare da tsoro ko cutarwa ba.
A cewarta, an ba da tallafin ne ta hanyar sabon tsarin kula da makarantun yara tare da bayar da tsaro.