Gwamnatin Nijeriya ta samu lamunin karbo bashin dala miliyan 134 daga bankin raya Afirka

 




Gwamnatin Nijeriya ta samu lamunin karbo bashin dala miliyan 134 daga bankin raya Afirka 


Gwamnatin Nijeriya ta samu lamuni domin ciyo bashin da ya kai dala miliyan 134 daga bankin raya Afirka domin bunkasa fannin noma ta hanyar samar da iri da hatsi ga manoma a kasar.


Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban jami’in yada labarai na ma’aikatar noma da samar da abinci, Anthonia Eremah ta fitar a Abuja, kamar yadda jaridar Daily Nigeria ta rawaito.


Ministan ma'aikatar Abubakar Kyari wanda ya bayyana haka a yayin kaddamar da noman rani na shekarar 2024/2025 a Calaba babban birnin jihar Cross River, ya ce bashin zai taimaka matuka wajen samar da abinci a kasar.


Ya kara da cewa tuni gwamnatin tarayyar Nijeriya ta sanya dokar ta-baci kan samar da



abinci.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp