Ministan Lafiya Farfesa Pate |
Ministan lafiya da walwalar al'umma Farfesa Ali Pate ya ce gwamnatin tarayya ta raba Naira biliyan 45 ga jihohi domin karfafa cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko.
Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a yayin wani taron hadin gwiwa na shekara ta 2024 da akai a Abuja.
Ya ce Naira biliyan 45 da aka raba wa cibiyoyin kiwon lafiyar zai shafi al’umma kai tsaye, inda ya kara da cewa sama da cibiyoyin dubu 8,000 suka amfana da kudade tare da kayan aiki domin ci gaba da duba marasa lafiya.
Farfesa Pate ya ce sama da cibiyoyin kiwon lafiya matakin farko 2,600 ana gab da farfado da su, kuma ana da shirin bunkasa wasu ƙarin 2,000. Ministan ya bayyana kokarin ma’aikatar lafiya, inda ya bayar da rahoton cewa sama da ma’aikatan ta 40,000 ne aka horas da su, wanda aka yi niyyar su kai 120,000.