Gwamnatin Nijeriya ta ba da tallafin kudi ga masu kananan kasuwanci a jihar Ebonyi

 

Bankin masana’antu BOI, ya ce akalla ‘yan kasuwa sama da 14,776 ne daga jihar Ebonyi suka ci gajiyar shirin ba da tallafin da gwamnatin tarayya ta kaddamar  a jihar.


Chukwudi Asiegbu, manajan BOI a Ebonyi ne ya bayyana hakan a yayin wani taron majalisar gari kan sakamakon shirin bayar da tallafin a ranar Juma’a a Abakaliki.


Asiegbu ya ce kowane dan kasuwa daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin an ba shi Naira 50,000 wanda jimilla kudin sun kai Naira miliyan 738.8.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp