Gwamnatin Nijar ta kai dan jarida Serge Mathurin gidan fursuna

 



Hukumomin mulkin soji na Nijar sun tisa-keyar dan jarida Serge Mathurin zuwa gidan yarin Birnin N'gaouré da ke cikin jihar Dosso.


A ranar Litinin din ta gabata ce aka gurfanar da dan jaridar dan asalin kasar Côte d'Ivoire a gaban kotu kan zargin shi da yi wa kasar Nijar zagon kasa don cin amanar kasar 


A kwanakin baya dai dan jaridar ya yi batan dabo da shi da motar shi bayan ya kira mai dakinsa ya ce zai amsa kiran jami'an tsaro.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp