Gwamna Ahmad Aliyu Sokoto zai fara biyan kudin gudanarwa na wata wata naira N200,000 ga kowane shugaban makarantar sakandare a jihar.
Wannan tsarin zai fara aiki ne daga watan daya na sabuwar shekarar 2025.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wurin taron jin ra'ayin jama'a kan kasafin kuɗin shekara ta 2025.