Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani |
Kananan Yara 39 daga Jihar Kaduna, wadanda a baya gwamnatin tarayya ta tsare su an sada su da iyayen su.
Taron ya gudana ne a ranar Larabar da ta gabata a dakin taro na Gidajen yara da ke kan titin Katuru a Kaduna, inda aka bai wa kowane yaro Naira 100,000 da kuma wayar salula kirar Itel A18s a wani bangare na shirin dawo da su.
Gwamna Uba Sani wanda sakataren gwamnatin jihar Kaduna Dr. Abdulkadir Muazu Meyere ya wakilta ya bada tabbacin ci gaba da tallafawa yaran yayin da suke komawa cikin al'umma.
Ya kuma jaddada kudirin gwamnati na samar da abubuwa da kuma karfafa musu gwiwa don taimaka musu su girma su zama ‘yan kasa masu kishin kasa, masu bin doka da oda.
Meyere ya bayyana cewa gwamnan ya umarce shi da ya karbi takardun shaidar kammala karatunsu, tare da shirin bayar da tallafi daban-daban da suka hada da jarin fara kasuwanci, horar da su sana'o'i, da samar musu da ayyukan yi.
Ya kuma ce gwamnati za ta sanya ido kan kowane yaro, tare da bayar da taimako bisa la’akari da halayensu, don tabbatar da bin diddigin da abubuwan da suke yi a cikin Al'umma.