Kwamitin da gwamnatin Edo ta kafa domin kwato kadarorin gwamnati ya ce sama da motoci 200 mallakin jihar ne suka bace.
Shugaban kwamitin Kelly Okungbowa ya bayyana hakan ga manema labarai a garin Benin, babban birnin jihar Edo a ranar Juma’a.
Ya ce tuni kwamitin ya gano uku daga cikin wadannan motoci kasa da kwana guda da suka fara kaddamar binciken.
A cewarsa, an kuma gano buhunan shinkafa da garrin kwaki da aka yi niyyar za a raba na tallafi a jihar a daya daga cikin motoci uku da aka
gano.