Gwamnan Kebbi Nasir Idris |
Gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris ya ba da umurnin kama wasu mutane da ake zargi suna da hannu a harin da aka kai wa wasu fulani biyo bayan harin da kungiyar Lakurawa ta kai Mera
A wata ziyarar jaje da ya kai garin Mera dake karamar hukumar Augie, gwamnan yayi Allah wadai da harin ramuwar gayya wanda yayi sanadiyar halaka wasu Fulani guda shida.
Rahotanni sun nuna cewa an kai harin ne kan Fulanin da ake zargin suna da hannu a harin Mera na farko, inda ‘yan ta’addan Lakurawa suka kashe mutane 17.
Da yake jawabi ga mazauna yankin da lamarin ya faru Gwamnan ya nuna damuwar sa bisa faruwar lamarin, inda ya ce, ya bayar da umarnin a kamo wadanda ke da hannu wajen harin da aka kai wada Fulanin da ba su ji ba ba su gani ba da sunan ramuwar gayya.
Gwamnan ya jaddada cewa bai kamata mutane su dunga daukar doka a hannunsu ba, ya kuma bukace su da sukai rahoto ga jami'an tsaro da zarar suka ga wani abu da basu amince da shi ba