Gwamnan Jihar Kano ya roki kungiyar likitoci ta kasa reshen jihar da su janye daga yajin aiki da suka tsunduma yi

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf


Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga kungiyar likitoci ta Nijeriya reshen jihar da ta dakatar da yajin aikin da ta ke yi domin kaucewa jefa rayukan al’ummar Kano sama da miliyan 20 cikin hadari.


Daily Trust ta ruwaito cewa Gwamna Yusuf ya kafa wani kwamiti domin bincike kan zargin cin zarafin da kwamishiniyar jin kai ta jihar, Amina Abdullahi HOD,ta yi wa wata likita a ranar Litinin a asibitin kwararru na Murtala Muhammed da ke Kano.


Kungiyar likitocin ta bai wa gwamnatin jihar wa’adin awanni 48 da ta kori kwamishinan jin kai, kuma ta sha alwashin ci gaba da yajin aiki , idan har gwamnati ta gaza biya mata bukatar ta.


Sai dai gwamnan da ya ke mayar da martani kan lamarin a yayin wani taron manema labarai da akai kai tsaye a gidan gwamnatin jihar ya bayyana rashin jin dadin sa kan matakin da kungiyar ta dauka bayan wata rashin fahimta juna da aka samu tsakanin tsakanin su.


Gwamnan ya jaddada cewa kungiyar za ta iya baiwa kwamitin binciken damar gudanar da bincike kan lamarin tare da daukar kwakkwaran mataki, maimakon dai na ayyukan su hakan zai taba wa'yanda basu ji ba basu gani ba a jihar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp