Gwamna Kano Abba Kabir Yusuf ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa nuna tausayi da ya yi ga 'yan Nijeriya

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf


Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa amsa kiran da jama’a suka yi masa tare da sakin yara 76 da aka tsare, wadanda aka kama bayan zanga-zangar watan Agustan 2024.


A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a Talatar nan, Gwamnan ya nuna matukar jin dadinsa da tausayin da shugaban kasar ya nuna, wanda ya bayyana shi a matsayin wani gagarumin abin alfahari ga matasan jihar Kano.


Gwamna Abba ya godewa shugaba Tinubu bisa fahimtarsa ​​da kuma baiwa yaran dama.Yara 76 da aka tsare saboda zanga-zangar da aka yi a watan Agusta, za a dawo da su Kano inda za a duba lafiyarsu tare da samun kulawar da ya dace kafin a sada su da iyayen su.


Gwamna Yusuf ya kuma ba da tabbacin cewa za a mayar da yaran cikin al’umma da kuma shigar da su makarantu, tare da samar musu da damar sake gina rayuwarsu.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp