Rikicin jam'iyyar NNPP a jihar Kano ya sake daukar wani sabon salo bayan da Gwamna Abba Yusuf ya yi fatali da wasu tarurruka da kuma kin amsa kiran ubangidansa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
A cewar jaridar Daily Nigerian wannan dai ya samo asali ne tun bayan bullen wata kungiya mai suna Abba Tsaya da Kafarka yayin da kiraye-kiraye daga ciki da wajen jam’iyyar ke kara ta’azzara na neman gwamnan ya samu ‘yancin kai daga ubangidan nasa.
Haka kuma an zargi sakataren gwamnatin jihar, Baffa Bichi da kwamishinan sufuri na jihar, Mohammed Diggol da kwamishinan ilimi Umar Doguwa da Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, sanata Kawu Sumaila, da dan majalisa, Ali Madaki da wasu 'yan majalisar dokokin jihar Kano.
Wannan dai na zuwa ne bayan da a ranar 1 ga watan Nuwamba, wata babbar kotun jihar Abia ta ba da umarnin mayar da ikon jam’iyyar ga tsohon shugaban ta Boniface Aniebonam.