Gawar tsohon babban hafsan sojin kasa na Nijeriya, Janar Taoreed Lagbaja ta isa Nijeriya
An sauke gawar ne filin jiragen sama na Murtala Muhammad da ke Lagos da misalin karfe tara na sanyin safiyar Alhamis, inda ake sa ran yi wa marigayi Taoreed Lagbaja sutura a ranar Juma'a.