Buhun shinkafar waje ya doshi naira dubu 100 a sassan Nijeriya


Farashin buhun masara na neman zama gagara badau musamman ga masu karamin karfi a kasuwar Mile 12 International Market Legas a kudancin Nijeriya, inda a makon nan ake sayar da buhun tsohuwar masara N100,000 cif, yayinda ita kuwa sabuwar ake saidawa N90,000, sai dai a makon jiya N95000 aka sai da buhun tsohuwar masara, sai kuma sabuwar aka sai da N75000 a makon da ya wuce.

To a kasuwar Dawanau jihar Kano, N64000 ake sayar da buhun masara a satin nan mai ƙarewa.

A wannan mako farashin masara bai sauya ba a kasuwannin jihar Adamawa, ta na nan a kan N67000, yadda aka saida a makon daya shude.

Hakazalika, a kasuwar Mai'adua jihar Katsina, N70,000 daidai aka sai da buhun masara a makon jiya, to a makon nan ma haka ake saidawa.

A kasuwar Dandume jihar Katsinan N57000- 65000 ake sai da buhun masara a satin nan.

Da DCL HAUSA ta leka kasuwar Giwa jihar Kaduna kuwa, ta taras cewa an samu ragin N4000 kan farashin buhun masara na makon jiya da aka saya N68000, a makon nan kuwa ake saidawa N64000.

Masarar tafi sauki a kasuwar Saminaka jihar Kadunan da ake saidawa N54000-55000 a satin nan, amma haka farashin yake a makon daya gabata.

Ita kuwa Shinkafar Hausa tafi sauki a kasuwar Mai'adua jihar Katsina da ake saidawa N137-138,000 a satin nan, amma a makon daya shude N135000 aka sai da buhun.

A kasuwannin jihar Adamawa N140-145000 ake sayar da buhun shinkafa 'Yar gida a satinnan, bayan da a makon jiya aka sai da N138,000.

N150,000 ake sayar da buhun shinkafa 'Yar gida a kasuwannin jihohin Kano da Legas a satin nan, sai dai farashin ya bambanta a makon jiya, inda a kasuwar Mile 12 International Market Legos aka sai da buhun N147000.

A kasuwar Giwa jihar Kaduna N155000 ake sai da shinkafar Hausa a satin nan,sai dai a makon jiya N140,000 aka sai da buhun, an samu karin N15000 kenan a mako ɗaya.

To a Dandume jihar Katsina N140,000-160,000 ake sai da buhun shinkafar Hausa a wannan satin, bayan da a makon jiya aka sai da N140-155000.

Sai kuma Saminaka jihar Kaduna ake sai da buhun shanshara na Shinkafa N49000-50,000, haka farashin yake a makon daya gabata. 

A bangaren Shinkafar waje kuwa, ta fi tsada a kasuwar Dawanau jihar Kano inda ake saidawa N105,000 a wannan sati.

Sai kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa ake sayar da buhunta N90-95000 a makon nan, bayan da a makon jiya aka sai da N90000.

Sai kuma mu nausa kasuwar Giwa jihar Kaduna da ake sai buhun Shinkafar 'yan gayu N90,000 a wannan sati, haka farashin yake a makonni biyu na watan Nuwamba na shekarar 2024.

To a kasuwar Mile 12 International Market, ana sayar da buhun shinkafar bature N85000, yayinda a makon daya wuce aka sai da N80,000, an samu karin N5000 kan farashin makon daya gabata.

Can a kasuwar Mai'adua jihar Katsina, an sai da buhun shinkafa 'yar gwamnati kan kuɗi N83000 a makon daya gabata, sai a makon nan ake saidawa N84000.

Sai dai, a kasuwar Dandume jihar Katsinan, N75000 ake sai da buhunta a satin nan, haka nan aka sai da makon daya shude.

Yanzu kuwa sai mu leka bangaren Wake, ga masu cin garau-garau ko kosai ko dai alala a gyara zama don farashin wake na makon nan.

Farashin tsohon waken ya fadi a kasuwar Mile 12 International Market Legas a wannan mako da ake saidawa N220,000, bayan da a makon jiya aka sai da N260,000, sai dai farashin sabon bai sauya daga yadda aka sai da a makon jiya, N180,000.

A kasuwannin jihar Adamawa N125000-130,000 ake sai da buhun farin wake kanana a makon nan.

N120,000 ake sai da buhun wake a kasuwar Mai'adua jihar Katsina a wannan mako, haka nan aka sai da makon daya wuce.

An samu sauƙin N20,000 kan farashin wake a kasuwar Giwa jihar Kaduna da ake saidawa N140,000 a satin daya shuɗe, amma a wannan sati N120,000 ake sai da buhunsa.

A kasuwar Dandume jihar Katsina N90,000-140,000 ake sayar da buhun wake a satin nan da ke dab da ƙarewa.

Sai kuma mu ƙarƙare farashin wake da kasuwar Saminaka jihar Kaduna, inda ake sai da buhun kananan wake 110,115 - 120,000 a makon nan.

Taliyar Spaghetti tafi sauki a kasuwar Mai'adua jihar Katsina wanda ake sai da Kwalinta N19300 a makon nan, a makon jiya kuwa aka sai da N19200.

Sai dai a kasuwar zamani da ke jihar Adamawa farashin na nan kamar na makon jiya da aka sai da N19700.

An samu ragin N500 kan farashin Kwalin taliya a kasuwar Giwa jihar Kaduna da aka sai da N20,500 a makon daya wuce, sai a makon nan ake saidawa N20,000 cif, yayinda ita kuwa kasuwar Mile 12 International Market Legos aka samu karin ₦500 kan farashin makon jiya da aka sai da N20,000, sai kuma makon nan ake saidawa N20500.

Ita ma kasuwar Dawanau jihar Kano N20500 ake sai da kwalin taliya a wannan sati.
  
Taliyar tafi tsada a kasuwar Dandume jihar Katsina, wanda ake Saidawa N21,000.

Alkhaluman da hukumar kididdiga ta kasa NBS ta fitar na nuna cewar hauhawar farashin kayan abinci ya kai kashi 33.88 a watan Oktoban 2024.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp