Farashin matatar Fatakwal ya fi tsada akan na matatar Dangote da naira 75


Kungiyar masu sarin mai ta Najeriya PETROAN, ta ce farashin fetur a matatar Fatakwal da ta soma aiki a wannan Talata ya fi na matatar Dangote tsada da naira 75.

Jami'in yada labarai na kungiyar Dr. Joseph Obele ne ya bayyana haka a lokacin bude matatar wadda za ta rika tace ganga 60,000 a kowace rana, inda ya ce farashin matatar Dangote naira 970 ne, yayinda a matatar gwamnati ke sayarwa a 1,045.

Dr Obele, ya bayyana damuwa akan yadda banbancin farashi zai iya kawo matsala ga kokarin da ake yi na daidaita farashin man fetur a fadin kasar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp