Wani sabon rahoto da hukumar kididdiga ta Nijeriya NBS ta fitar, ya nuna cewa farashin kayayyaki ya karu a cikin watan Oktoba zuwa kashi 33.88, daga kashi 32.70 da ya kai a watan Satumban 2024.
A cewar NBS, hakan na nufin an samu karin farashin kashi 1.18.
A cewar jaridar Punch, farashin kaya a Nijeriya na ci gaba da tashi da sauka a wannan shekara, inda a watan Yuni sai da farashin ya kai kashi 34.19 karo na farko cikin shekaru 30.