Hukumomi a kasar Rasha sun musanta labarin da wasu kafafen yada labarai na kasar Amurka suka yada cewa, Shugaba Vladmir Putin da zababben Shugaban Amurka Donald Trump sun yi wata zantawa ta wayar tarho a karshen makon da ya gabata.
Mai magana da yawun fadar Kremlin Dmitry Peskov, ya shaidawa manema labarai cewa babu wata tattaunawa da shugabannin suka yi.
Jaridar Washington Post ta ruwaito cewa, Trump ya shaidawa Shugaba Putin anniyar fadar White House na kawo karshen yaki tsakanin Rasha da Uk.raine.