DSS sun cafke ɗan siyasa da buhunan kudi da ake zarginsa da sayen kuri'un masu zabe a Ondo

 



Jami'an hukumar tsaron sirri ta DSS a Nijeriya sun cafke wani dan siyasa da manyan buhunan kudi da ake zarginsa da sayen kuri'a a zaben jihar Ondo


An kama mutumin wanda ake zargin da buhunan kudi guda biyu wadanda ake zargin na janyo hankalin masu kada kuri’a a zaben.


An kama shi ne a mazaba ta 4, rumfa mai lamba 007 da take a wajen makarantar St. Stephen’s Primary School, Akure, Jihar Ondo da misalin karfe 9 na safe a ranar zabe.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp