Matatar dangote ta bayyana cewa farashin man ta ya fi wanda ake shigowa da shi daga kasashen waje arha ta re da ayyana cewa za ta rika sayar da litar man fetur kan Naira 990.
Hakan dai na a cikin wani martani da ta maida wa wasu ‘yan kasuwa da su ke cewa man fetur din waje ya fi arha fiye da wanda ake kawowa daga matatar Dangote.
Daidai matatar Dangote a cikin wata sanarwa da Babban Jami’in Kula da kasuwanci da Sadarwa, Anthony Chiejina, ya bayyana ikirarin da IPMAN da sauran ‘yan kasuwa suka yi a matsayin wanda ba haka yake ba