Dan wasan Najeriya Ademola Lookman ya shiga cikin jerin fitattun yan wasan kwallon kafa da su ka hada da Lionel Messi, da Cristiano Ronaldo, da Kylian Mbappé, da kuma Erling Haaland, wadanda aka zaba domin karbar kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na shekara ta 2024.
Wannan dai wani bangare ne na bukukuwan bada lambar yabo na shekara-shekara na Globe Soccer wanda Hukumar Wasannin Dubai ke shiryawa.
Sanarwar da Globe Soccer Awards su ka wallafa a shafin X a wannan Alhamis, ta ce dan wasan Najeriya Ademola Lookman na cikin wadanda aka zabo domin cin kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya na 2024.