Dan majalisar tarayya na Katsina ya share wa al'ummarsa hawaye, bayan gina musu titin da suka jima suna rokon a gina musu



Dan majalisar tarayya da ke wakiltar karamar hukumar Katsina a majalisar wakilai ta tarayya, Hon Sani Aliyu Danlami ya share wa wasu al'ummar cikin kwaryar birnin Katsina hawaye, a wani aikin titin da suka jima suna rokon a yi musu, amma abin ya ci tura.


Titin da dan majalisar ya gyara shi ne wanda ya tashi daga Masallacin Juma’a na GRA ya bi ta Gidan Dawa ta zarce zuwa makabarta har ta bulle zuwa titin Ring Road na Liyafa.


Kasa da wata daya dai dan majalisar tarayyar Sani Aliyu DanLami ya kaddamar da aikin, amma har an kammala shi.


Aikin dai, na daga cikin ayyuka uku na tituna da dan majalisar tarayya Hon Sani Aliyu DanLami yake gudanarwa a halin yanzu a karamar hukumar Katsina, inda yake wakilta.

Sauran ayyukan hanyar sun hada da wadda tashi daga bayan gidan gwamnati a Modoji sai wadda ta bi ta bayan Customs Base a cikin GRA da kuma Layout akan titin Dr Garba Shehu Matazu.


Ayyukan na daga cikin kokarin da Sani Aliyu DanLami yake yi na inganta rayuwar al'ummar karamar hukumar katsina.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp