Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayar da umarnin sakin duk wasu kananan yara da aka kama da kuma tsare su saboda zanga-zangar tsadar rayuwa a Nijeriya.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Litinin
Muhammad Idris ya ce shugaban kasar ya umurci babban lauyan gwamnatin tarayya, Lateef Fagbemi, da ya gaggauta fara aikin ganin an sako yaran domin haduwa da iyalansu.
An kuma kafa wani kwamiti da zai duba hanyoyin da aka bi wurin kama su tare da tsare su domin yi masu adalci