Cutar kwalara ta yi ajalin mutane 25 a Sokoto, yayin da 15 ke kwance a asibiti

 


Cutar kwalara ta yi ajalin  mutane 25 a Sokoto, yayin da 15 ke kwance a asibiti


Akalla mutum 25 ne aka tabbatar da mutuwar su daga cikin  mutane 1,160 da su ka kamu da cutar Kwalara a jihar Sokoto. 


Kwamishiniyar lafiya ta jihar Asabe Balarabe, ta bayyana haka a ranar Litinin a lokacin da take zantawa da manema labarai.


Majiyar DCL Hausa wato Jaridar Punch, ta ambato kwamishiyiyar na cewa zuwa yanzu mutum 15 a ke ci gaba da kulawa da su a asibiti, a kananan hukumomin Sokoto ta Arewa da Silame da kuma Kware.


Yayinda gwamnatin jihar ke ci gaba da kokarin dakile yaduwar cutar, a cewar Hajiya Asabe Balarabe.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp