Ciwon suga ya yi sanadin rasa rayukan sama da mutane 55,000 wannan shekarar a Nijeriya


Kwararre kan ciwon suga da ake kira Diabetes a turance, Farfesa Olufemi Fasanmade na asibitin koyarwa ta jami'ar jihar Lagos ya ce sama da mutane 55, 000 ne su ka mutu sanadiyar cutar a wannan shekara.

Ya bayyana hakan ne a yayin da 'yan jarida ta yanar gizo kan cutar 'diabetes' suke yi masa tambayoyi, wanda kamfanin magani na Novo Nordisk ya shirya.

Farfesa Fasanmade ya ce a shekara ta 2021 mutane 48,375 suka mutu, a shekara ta 2022 kusan mutane 50,000 suka mutu yayinda a shekara ta 2023 kusan mutane 53,000 su ka mutu sanadiyar cutar suga.

A cewar kwararren daga cikin mutum miliyan 24 da ke fama da cutar a Afrika, mutum miliyan 4 daga Nijeriya suka fito kuma ana hasashen cewa yawan su zai karu nan da shekaru 20.


 

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp