A daidai lokacin da bikin kirsimeti ke ƙara karatowa, farashin wasu daga cikin kayan abinci na kara tashi, yayin da wasu kuwa farashin su ke sauka a kasuwannin jihohin Nijeriya.
Shinkafar Hausa ta fi sauki a kasuwar Mai'adua da ke jihar Katsina a yankin arewa maso yammacin kasar da ake saidawa N138,000 a makon nan, inda a makon jiya aka sayar kan kudi N137,000.
Sai dai a kasuwannin jihar Adamawa da DCL Hausa ta tuntuɓa farashin buhun shinkafa 'yar gida bai sauya ba dana makon daya gabata, wanda aka saida shi kan farasgin N140,000- 145,000.
N155000 ake sai da buhun shinkafar hausa a kasuwannin Giwa ta jihar Kaduna da Mile 12 International Market Legas a satin nan da ke shirin karewa, sai dai farashin ya sha banban a kasuwannin a makon jiya, inda a kasuwar Mile 12 International market aka sayar da buhun kan N147,000, amma farashin bai sauya ba a kasuwar Giwa jihar Kaduna da ake saidawa N155,000.
Hakazalika farashin buhun shinkafa bai sauya tufafi ba a kasuwar Dandumen jihar Katsina da aka sai da N140,000-160,000 a makon daya shude, kuma haka abin yake a makon nan da muke ciki.
A kasuwar Dawanau jihar Kano ma dai farashin shinkafar hausa bai sauya dana makon jiya ba, wanda aka sai da N150,000.
Ita kuwa shanshara na shinkafar N50,000-55,000 ake sai da buhunta a kasuwar Saminaka jihar Kaduna a wannan sati, bayan da a makon jiya aka sai da N49,000-50,000, an samu karin N5000 a mako daya kenan.
A bangaren Shinkafar Bature kuwa, ita tafi tsada a kasuwar Dawanau jihar Kano wanda aka sai da N105000 a satin daya wuce, haka kuma ake saidawa a wannan sati.
A kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa N87,000-90,000 cif ake sai da buhunta a wannan mako,bayan da a makon jiya aka sai da N90,000-95000.
An samu karin N5000 kan farashin shinkafar a kasuwar Mai'adua jihar Katsina a satin nan da ake saidawa N88,000,amma a makon daya wuce N83000 aka sai da buhun ta.
Haka ma a kasuwar Dandume jihar Katsinan farashin yayi tashin Goron zaɓi a makon nan, wanda ake saidawa N85000,sai dai a makon jiya N75000 aka sai da buhun,karin N10,000 kenan a mako guda.
N87000 ake sai da buhun shinkafar bature a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas a wannan sati,yayinda a makon jiya aka sai da N85000.
Farashin shinkafar ya kusan rufa N100,000 a kasuwar giwa jihar Kaduna da ake saidawa N98,000 a satin nan da ke mana bankwana.
To bari mu je ga bangaren masara, inda buhun tsohuwar masara ma yafi tsada a kasuwar Mile International Market Legas wanda ake sai da buhun N105000 a wannan sati, sai kuma sabuwar masara ake saidawa N90,000 a makon nan, haka nan farashin yake a makon jiya.
A kasuwar Dawanau jihar Kano ma farashin buhun masara bai sauya ba dana makon jiya wanda aka sai da N64000.
Sai kasuwannin jihar Adamawa da DCL Hausa ta tattara bayanai inda ake sai da buhun sabuwar masara N60,000-67,000 a wannan mako, amma dai farashin ya danganta da girman buhun.
An samu ragin N1000 guda kan farashin masara a kasuwar Mai'adua jihar Katsina, inda a makon nan ake sai da buhun N69000, bayan da a makon daya gabata aka sai da N70,000 daidai.
A can a kasuwar Dandume jihar Katsinan N60,000-65000 ake sai da buhun masara a makon nan,sai dai,a makon jiya N57000-65000 aka sai da buhunta.
A kasuwar Saminaka jihar Kaduna,N55000-57000 ake sai da buhun masara a satin nan,amma a makon jiya kuwa N54000-55000 aka sai da.
Ita ma kasuwar Giwa jihar Kaduna an samu saukin N1000 kan farashin makon jiya wanda aka sai da N64000,a makon nan kuwa ake saidawa N63000.
Farashin tsohon wake kuwa na ci gaba da sauka a kasuwar Mile International Market da ke jihar Legas,inda a makon nan ake sai da buhun N210,000,bayan da a makon jiya aka sai da N220,000 a kasuwar.
Sai kasuwannin jihar Adamawa ake sai da buhun kananan wake N120,000 a wannan mako,bayan da a makon jiya aka sai da N125000-130,000.
A kasuwar Dandume jihar Katsina N90,000-140,000 ake sai da buhunsa a makon nan, haka farashin yake a makon jiya.
Farashin kananan wake bai sauya zani ba a kasuwar Saminaka jihar Kaduna, wanda ake sai da buhun N110,000-120,000
To a kasuwar Giwa jihar Kaduna N115,000 ake sai da buhun wake a satin nan da ke mana bankwana.
A bangaren taliya kuwa, kwalin taliyar tafi tsada a kasuwar Dandume jihar Katsina wanda ake sai da ta N22,000 a satin nan,bayan da a makon jiya aka sai da N21,000.
A kasuwar Dawanau jihar Kano N19300 ake sai kwalin taliyar Spaghetti a wannan mako,amma a makon daya gabata N21,000 aka sai da kwalin.
Farashin kwalin taliya bai canza ba dana makon jiya wanda aka sai da N19700 a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa.
An samu karin N200 kan farashin taliyar Spaghetti da ake saidawa N19500 a wannan sati,bayan da a makon jiya aka sai da N19300.
Sai kasuwar Mile 12 International Market Legas ake sai da kwalinta N21,000 a makon nan,yayinda a makon daya gabata aka sai da N20,500.
Ita ma kasuwar Giwa jihar Kaduna farashin bai sauya ba dana makon jiya da wanda aka sai da N20,000 cif.