Babban Bankin Nijeriya CBN ya kara kudin ruwa zuwa kaso 27.50


Babban bankin Nijeriya CBN ya kara kudin ruwa daga kaso 27.25 zuwa kaso 27.50, a kokarin da yake na magance matsalar hauhawar farashin kayayyaki.

Wannan ya biyo bayan taron da kwamitin harkar kudade na bankin ya gudanar.

Gwamnan CBN ya ce taron ya amince da kara kudin ruwa da 0.25 wanda ya sa kudin ruwa ya kai kashi 27.50.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp