APC ta lashe zaben Gwamnan jihar Ondo


Hukumar zabe a Nijeriya ta bayyana gwamna Lucky Aiyedatiwa a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Ondo da kuri'u 366,781.

Shi kuwa 'dan takarar jami'iyyar PDP kuma tsohon mataimakin gwamna Agboola Ajayi ya samu kuri'u 117,845.

Jam'iyyar Labour Party da ta samu kuri'u 1,162 kamar yadda RFI Hausa ta rawaito.

Shugaban jami'ar gwamnatin tarayya dake Lokoja kuma baturen zaben Farfesa Olayemi Akinwunmi ne ya gabatar da sakamakon zaben a gaban 'yan jarida bayan kammala tattara alkaluman kananan hukumomi 18 wadanda aka tabbatar da nasarar Aiyedatuwa a cikin su baki daya.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp