Mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima |
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya ce an yi asarar sama da Naira biliyan 300 a zanga-zangar #EndBadGovernance da ta gudana a fadin kasar cikin watan Agusta.
Da yake jawabi a fadar shugaban kasa da ke Abuja, yayin da yake karbar yaran da aka kama yayin zanga-zangar bayan an sako su bisa umarnin shugaban kasa Bola Tinubu, Shettima ya ce an yi hasarar akasarin dukiyoyi da harkokin kasuwanci a yayin zanga-zangar.
Ya ce duk da hujjojin da ake da su a kan yaran, shugaba Tinubu ya ba da umarnin a sake su ne saboda shi shugaba ne mai kula da bukatun al’umma.
Shettima ya kuma yi kira ga gwamnoni da sauran jami’an gwamnati da su yi abinda ya kamata wajen sanya matasan masu amfani a cikin al’umma.