Tsohuwar ministar kudi ta Nijeriya kuma Darakta Janar ta kungiyar cinikayya ta duniya Dr Ngozi Okonjo-Iweala, ta sake komawa kan muƙamin karo na biyu.
Wa'adin mulkin nata na wasu shekaru 4 zai soma ne daga ranar 1 ga watan Satumban 2025.
A cikin wani bayani da ta fitar wannan Jumu'a, Okonjo-Iweala ta godewa membobin kasashen 166 bisa goyon baya da amicewar da suka dora mata.
📸 World Trade Organization