Kimanin mutun 76 masu zanga-zangar tsadar rayuwa da ake tsare da su suka isa gaban kotu a Abuja.
A cewar jaridar Punch masu zanga-zangar galibin su dai yara kanana ne kuma akwai yunwa tattare da su da rashin abinci mai gina jiki.
An kama su ne tare da tsare su a zanga-zangar da aka yi a fadin kasar a ranakun 1 zuwa 10 ga watan Agusta wanda ya samo asali daga matsalar tabarbarewar tattalin arziki da ya sa ‘yan Nijeriya da dama suka fito kan tituna suna bayyana kokensu.