Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya sake nada mukamai guda biyu na mutanen da za su rika magana da yawun fadar shugaban kasa.
Wata sanarwa da Hadimin shugaban ƙasa kan yaɗa labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce yanzu ba mutum daya ne zai riƙa magana da yawun shugaban ba.
Ko baya ga shi Bayo Onanuga, shugaba Tinubu ya amince da naɗa Mista Sunday Dare da kuma Daniel Bwala a matsayin masu ba shi shawara akan yada labarai da harkokin sadarwa.
Wannan dai wani mataki ne da ake kallo garambawul da gwamnatin ke yi, a cewar jaridar Premium Times.