An kori kungiyar Lakurawa daga Nijeriya - Sanata Aleiro


Sanata Adamu Aleiro mai wakiltar Kebbi ta tsakiya a majalisar Dattawa ya ce sojojin Nijeriya sun kori sabuwar kungiyar nan ta Lakurawa zuwa Jamhuriyar Nijar.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a yau jumu'a, Sanatan ya ce wannan nasarar ta samu ne bayan da ministan tsaro Abubakar Badaru, da babban hafsan soji da sauran hukumomin tsaro su kaddamar wa Lakurawa.

A cewarsa, tun ranar 12 ga watan Nuwamba da sojoji suka isa yankin Sokoto da Kebbi su ke fatattakar yan bindigar, kamar yadda jaridar Dailytrust.

Aliero ya ce tuni da sojoji suka gargada yan ta'addar suka bar iyakar Nijeriya, inda ya ce yanzu ya ragewa sojojin Nijar su gama da su saboda na kasar ba zasu iya shiga Jamhuriyar Nijar domin yaki da su ne ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp