Hukumomin kasar Libya sun kama wasu 'yan Nijeriya 4 bisa zargin safarar miyagun kwayoyi kuma binciken lafiya ya nuna suna dauke da cututtuka masu yaɗuwa.
Wani bayani da kungiyar da ke kula da bakin haure wato Migrant Rescue Watch, ta wallafa a shafin X ta ce an kama mutanen a garuruwan Sabha da Bani Walid da ke kudancin birnin Tripoli.
Dukkanin waɗanda aka kama an hannun ta su ga hukumomin da suka dace domin ci gaba da bincike, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
Category
Labarai