An kama wani mutum da ake zargi yaudarar mutane a matsayin dan'uwa ga Sheikh Gadon Kaya a jihar Kano


Jami'an 'yan sandan Kano sun kama wani mutum da ake zargi da yaudarar mutane ta hanyar tura musu sakon kudi na bogi.

Ana kuma zargin mutumin mai suna Sunusi Aminu dake Kofar Nassarawa, da yin karyar cewa shi dan uwan sanannen malamin addinin musuluncinnan ne Sheikh Dr. Abdallah Usman Gadon Kaya domin samun yardar mutane a lokacin da suke kasuwanci, daga baya sai ya yaudaresu da sakon kudi na bogi a matsayin ya tura a asusun banki.

Wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce sama da mutane 20 sun gabatar da korafi akan mutumin bayan kama shi kuma ana zargin ya karbi kayan da suka kai naira miliyan 2.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp