An hallaka mutane 30 a wasu kauyukan jihar Benue

A kalla mutum 30 ne aka hallaka a wasu kauyukka dake kananan hukumomin Kastina-Ala and Logona jihar Benue.

Mazauna yankunan sun shaidawa jaridar Dailytrust cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da kuma safiyar Litinin.

Wani basaraken yankin ya ce wasu mayaka aƙalla 300 wadanda ake zargin ba a Nijeriya suke ba, suka kai wannan hari.

Ya ce a lokacin da suka zo jami'an tsaro sun yi iya kokarin su amma an ci ƙarfin su, sai da su ka samu dauki daga jirgin yaki kafin mayakan su arce, bayan kashe mutum 20.

Hakama wani harin da wasu makiyaya suka kai a karamar hukumar Kastina-Ala ya haddasa mutuwar mutane 10.

Jami'ar yada labarai ta rundunar 'yan sandan jihar Catherine Anene ta tabbatar da faruwar harin karamar hukumar Logo, sai dai ta ce mutum 5 aka tabbatar da mutuwar su zuwan yanzu.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp