An gufanar da wani dattijo dan kimanin shekaru 50 da haihuwa mai suna Gbenga Adeleke, a gaban kotun majistare dake Iyaganku a birnin Ibadan jihar Oyo bisa zargin satar abincin kaji mai nauyin 100kg wanda kudinsa ya kai naira 52,000.
Adeleke, ya musanta zarge-zargen da ake masa na hada baki wajen yin sata tare da wasu mutane, a cewar jaridar Dailytrust.
Alkalin kotun Majastare Mrs Olabisi Ogunkanmi, bayan sauraren karar ta bayar da belin wanda ake zargi akan naira dubu 50,000 tare da dage sauraren karar har sai ranar 27ga watan Fabrairun 2025.
Category
Labarai